Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (Nigeria Immigration Service) ta ja hankalin al’umma dangane da ɓullar wata ƙungiya mai suna “ACHAD Life Mission International” da ake zargi fa safarar mutane zuwa wajen ƙasar tare da raba yara da iyayen su.
- Da Ɗumi-Ɗumi: An sake samun ɓullar wata sabuwar ƙungiya mai hatsari a Najeriya
- Gwamnan Neja ya haramta wa manyan motoci hawa saman gadar Dikko
- Dokar Haraji: Matakin da gwamnoni su ka ɗauka bai wadatar ba- Sanata Ndume
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar 14 ga watan Janairun da mu ke ciki, ta ce ƙungiyar yanzu haka ta kafa hedikwata a Kaduna yayin da shugabanta, wani mai suna Mista Yokana, ke zaune a Jos na jihar Plateau.

Ita dai wannan ƙungiyar kamar yadda sanarwar ta ce ba ta yadda da addinin Musulunci ko Kiristanci ba, amma ta na yaɗa da’awar dawo da al’adar nahiyar Afirka tare da taimaka wa al’umma.