Daga Latifa Shuaibu Gani
Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya yi wa wani matashi Segun Olowookere afuwa, wanda aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon samunsa da laifin satar kaza a shekarar 2010.
Cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, kimanin mutane 53 ne gwamnan ya yi wa afuwa ciki har da Olowookere.
Labarin Olowookere ya zagaye gari a ƴan kwanan nan tun bayan wani hira da aka yi da iyayensa, waɗanda su ka bayyana cewa an kama ɗansu bisa laifin da bai aikata ba.
Wannan ya sa Gwamna Adeleke ya umurci Kwamishinan Shari’a na jihar da ya gudanar da bincike kan lamarin.