9.4 C
London
Wednesday, January 15, 2025

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan kuɗi har Naira miliyan 500.

Yayin zamanta na yau Jumma’a, kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Emeka Nwite ta nemi Yahaya Bello da ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa kafin samun belin, kuma su kasance su na zama a Abuja tare da gabatar da takardun kadarorinsu.

A farkon wannan makon ne dai kotun ta bada umarnin ajiye tsohon gwamnan a gidan yarin Kuje da ke Abuja bayan ta ƙi amincewa da buƙatar bayar da belinsa akamr yanda lauyoyinsa su ka nema, tare da ɗage sauraron ƙarar har sai ranar 29 ga watan Janairun 2025.

Ana tuhumar Yahaya Bello ne dai da karkartar da sama da Naira biliyan 100 a lokacin da ya ke kan kujerar gwamnan Kogi.

Sabbin Labarai
Labarai Masu Alaka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here