9.4 C
London
Wednesday, January 15, 2025

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnan Adamawa ya cire Lamiɗo a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan jihar

Majalisar dokokin jihar Adamawa ta amince da ƙudirin kafa wasu sabbin masarautu masu daraja ta daya a jihar, ƙudirin da a halin yanzu ya tsallake karatu na daya da na biyu a zauren majalisar dokokin jihar a ranar Litinin tare da samun amincewar majalisar na zama doka.

Sabuwar dokar masarautar wacce a yanzu take jiran amincewar Gwamna Ahmadu Fintiri, na zuwa ne kwanaki bayan da gwamnan ya amince da wata doka da ta ƙirkiro sabbin gundumomi 83 a ranar 4 ga Disamba.

Fintiri, a wata wasiƙa da ya aike wa ‘yan majalisar a ranar Litinin kamar yadda majiyar Hausa Daily Times wato Jaridar Premium Times, ya bukaci a amince da kudirin dokar.

Kudirin ya baiwa gwamnan ikon samar da ƙarin masarautu, da naɗa sarakuna ko kuma tsige su. Ana sa ran gwamnan zai bayyana sabbin masarautun bayan amincewa da kudirin

Sabuwar dokar ta cire Lamidon Adamawa Mustapha Barkindo daga mukaminsa na shugaban majalisar sarakunan Adamawa na dindindin.

Dokar ta ce kujerar za a rinƙa yin karɓa-karɓa da ita duk shekara a tsakanin dukkan sarakuna masu daraja ta daya.

Masana sun gano cewa dokar ta raunana tasirin sarautar Lamidon Adamawa, ta hanyar rage masa yawan ƙananan hukumomin da ke karkashinsa daga takwas zuwa uku.

Masarautar Lamiɗon Adamawa, ta haɗa da Ƙananan Hukumomi Hong, Song, Gombi, Fufore, Girei, Yola North, Yola South, da Mayo-Belwa. Sai an tabbatar da sabuwar dokar za a san ƙananan hukumomin da za su kasance a ƙarƙashinsa.

Sabbin Labarai
Labarai Masu Alaka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here