Hukumar gudanarwar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara da ke Ilorin ta yi ƙira ga mutanen da suka ajiye gawarwaki a dakin ajiyar gawa na asibitin da su kwashe su cikin makonni biyu.
Asibitin a cikin wata sanarwa da Shugaban Sashin Hulda da Jama’a, Yakub Aliagan, ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce ɗakin ajiyar gawarwaki na asibitin ya cika sakamakon gawarwakin da har yasu ba a san masu su ba.
Wani bincike ya gano cewa, gawarwakin dai sun kasance a dakin ajiye gawaki na asibitin da ma wasu manyan asibitocin jihar na tsawon lokaci, yayin da wasu daga cikinsu su ka haura shekaru goma a ajiye kuma galibinsu waɗanda aka ajiye ne daga wuraren da aka yi fashi da makami da kuma hadarurrukan mota.