Duk da ƙiraye-kirayen su ke yi wa ƴan Najeriya na su jure wa tsadar rayuwa da sauran matsalolin tattalin arziƙi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shatima, sun kashe wa kansu Naira Biliyan 1.7 a matsayin ihisani baya ga kuɗin albashi da su ke karba duk wata a shekarar 2024, kamar yadda binciken cibiyar ICIR mai binciken ƙwaƙwaf ya gano.
A cewar ICIR, wannan bisa ga bayanai ne cibiyar “GovSpend”, wata ƙungiya ce da ke bin diddigin abubuwan da gwamnati ke kashewa.
Naira biliyan 1.7 na iya biyan albashin ma’aikatan gwamnati 22,283 duk wata in aka yi amfani da sabon mafi ƙarancin albashin Najeriya na N77,000.
Kazalika, shugaban kasa da mataimakinsa, ciki har da uwargidan shugaban ƙasa, sun kashe Naira biliyan 6.8 wajen tafiye-tafiyen kasashen waje da kuma abubuwan da suka shafi makamancin haka a bana. Bayanan da majiyarmu ta ICIR ta ce ta samu a ranar 11 ga Oktoba na wannan shekara 2024, ta kama kudaden da gwamnati ta kashe har zuwa 15 ga Satumba.
Majiyar ta ruwaito cewa, gwsmnatin ta yi waɗannan kashe-kashen ne a cikin lokacin jama’ar ƙasar ke fama da matsanaicin matsin rayuwa a sanadiyyar tsare-tsaren da manufofin tattalin arziƙi na gwamnatin Shugaba Tinubu, ciki har da janye tallafin man fetur tare da karyewar darajar Naira.