7.3 C
London
Friday, October 4, 2024

Yan bindiga na neman babura 130 kafin su saki mata 26 da suka sace a jihar Neja

‘Yan ta’addan da suka yi garkuwa da mata 26 a garin Allawa na karamar hukumar Shiroro a jihar Neja sun fitar da wani faifan bidiyo dauke da biyu daga cikin wadanda suka kama. A cikin bidiyon, matan sun roki iyalansu da su kaiwa ‘yan ta’addan babura 130 da suka bukata domin a sake su.

Bidiyon mai tsawon dakika 30, ya nuna daya daga cikin matan da aka daure a jikin bishiya, tana rokon ‘yan uwanta da su kai kayan da masu garkuwar suka bukata. Da take magana da harshen Hausa, ta yi kira ga wani dan uwanta mai suna Abdulrahman da ya taimaka wajen samar da baburan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wani mazaunin garin Abba Usman ya tabbatar da cewa matan da aka bayyana a bidiyon na daga cikin mutane 26 da aka yi garkuwa da su a watan Fabrairun bana. Ya ce, tuni iyalan matan biyu suk ba da babura shida, amma yanzu masu garkuwa da mutane suna neman karin babura hudu kafin a sako su.

Usman ya kara da cewa iyalan sauran mata 24 sun sanar da ‘yan ta’addan cewa ba za su iya sayen karin baburan ba.

‘Yan ta’adda dai na bukatar babura biyar ga kowacce daga cikin matan guda 26, inda kowanne babur ya kai Naira miliyan biyu.

A halin da ake ciki, wata Kungiyar kabilar Gwari Gbenu Boknu Yakwo, ta yi kira ga gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da ya kori kwamishinan tsaron cikin gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi (mai ritaya) bisa zargin gazawa wajen magance matsalolin tsaro da ke kara tabarbarewa a garin Allawa da sauran yankunan karamar hukumar Shiroro ta jihar.

Sabbin Labarai
Labarai Masu Alaka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here