7.3 C
London
Friday, October 4, 2024

An yi wa marigayi Sarkin Gobir sallar Ga’ib bayan sallar Jumma’a a Sakkwato

Daga Mukhtar A. Halliru Tambuwal, Sokoto

Al’ummar musulmi da suka gabatar da sallar Jumma’a a masallacin Sahaba da ke Sakkwato sun gabatar da Sallar Ga’ib ga kisan gillar da aka yi wa uban ƙasar Sabon Birnin Gobir, marigayi Alhaji Isa Muhammad Bawa, jim kaɗan bayan idar da sallar Jumma’a da aka gudanar yau.

Limamin masallacin Dr Usman Riba, Mataimakin Kwamandan Hisba na Jihar Sakkwato ne ya jagorancin sallar, bayan ya yi bayanin cewa Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto mni, shugaban Cibiyar Da’awa ta Ahlilbaiti da Sahaba ne ya bada umurnin yin sallah, wanda ya bayyana ya halarcin yin wannan sallah, musamman duba da yadda aka yi kisan.

Limamin ya yi kira ga al’ummar Musulmi, Hausawa da Fulani, da su shiga taitaiyin su kar su yarda maƙiya su yi nasarar cimma burinsu na haɗa faɗa tsakanin musulmi Hausawa da Fulani. Limamin ya yi kira ga Gwamnati da Masarauta da sauran al’umma da su tabbatar da ganin an shawo kan matsalar.

Ya kuma yi ta’aziyya ga al’ummar musulmin kan wannan rashin, tare da addu’ar Allah Ya karɓi shahadarsa.

Sabbin Labarai
Labarai Masu Alaka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here