9.9 C
London
Friday, October 4, 2024

Ka zaɓi ko wace ƙasa cikin Afirka domin zama Jakada, Shugaba Tinubu ga Ganduje

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Shugaba Ƙasa Bola Tinubu ya bai wa shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje damar zaɓar kowace kasa daga Afirka domin zama jakada.

Idan mai karatu bai mance ba an nada Ganduje a matsayin shugaban jam’iyya mai mulki na kasa ne a ranar 3 ga watan Agusta, 2023, biyo bayan murabus din da Abdullahi Adamu ya yi.

Majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa, yanzu haka tinubu ya fara wakilta Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio domin ya isar da wannan sako ga Ganduje.



A cewar majiyoyin, Mista Akpabio ya shaida wa shugaban jam’iyyar APC na kasa cewa tayin jakadan shugaban kasar na da nufin ceto shi daga shari’ar cin hanci da rashawa da yake fuskanta a Kano a halin yanzu.

Sai dai majiyoyi na cikin gida sun ce Ganduje ya yi gunaguni lokacin da labarin ya iso shi, kuma ya ki amincewa da tayin shugaban kasar cikin dabara, yana mai bayanin cewa tuhume-tuhumen “tuggu ne kuma yawancin su karya ne” kuma zai ci nasara a shari’arsa a kotu.

Sabbin Labarai
Labarai Masu Alaka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here