9.9 C
London
Friday, October 4, 2024

Ku kula, an sake samun mutane 11 da suka mutu daga cikin garin Rogo a Sokoto da Kwara

Rahotonni daga jihar Sokoto sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 7 ‘yan gida daya a kauyen Runjin Barmo da ke gundumar Kajiji a karamar hukumar Shagari sakamakon cin garin rogo da ake zargin ba mai kyau bane.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in yada labarai na ma’aikatar lafiya ta jihar Sokoto, Nura Bello, a madadin kwamishiniyar lafiya Hajiya Asabe Balarabe, a yammacin Lahadin da ta gabata.

A cewar sanarwar, wadanda suka mutun sun hada da: Malam Abubakar (mai gidan), matarsa, A’ishatu Abubakar da ‘ya’yansu biyar.

A jihar Kwara ma, mutane hudu sun rasa ransu a irin hakan a garin Eruda kamar yadda Kwamishiniyar Lafiyar ta jihar Dr. Amina El-Imam ta tabbatar a taron manema labarai a Ilorin.

Kwamishiniyar ta ce, wadanda suka mutun ‘yan gida daya ne, Kaka da jikokinta wadanda suka mutu nan take bayan cin tuwon “Alubo”.

Hausa Daily Times ta ruwaito a ranar Lahadin da ta gabata faruwar irin wannan iftila’in a jihar Kogi, inda mutane 6 suka mutu a ranar Laraba ta makon joya, sannan aka sake samun wasu mutum 3 ‘yan gida daya da suma suka mutu a karamar hukumar Suleja a jihar Neja.

Sabbin Labarai
Labarai Masu Alaka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here