7.3 C
London
Friday, October 4, 2024

Mutane 6 sun mutu daga cin tuwon garin rogo…..

Mutane 6 sun mutu sakamakon tuka tuwon wani garin rogo da ake zargin gurbatacce ne a jihar Kogi.

Majiyar Hausa Daily Times ta jaridar Kogi Reporters ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Laraba da ta gabata a wani gida a unguwar Anyoke da ke gundumar Okunchi a karamar hukumar Adavi ta jihar.

Hoto Don Misali: Tushen rogo

Bayanai sun ce, mutane takwas ne iftila’in ya shafa wadanda kuma aka yi gaggawar garzayawa da su asibitoci daban-daban, sai a can ne shida daga cikinsu suka rasu.

Tuni dai gwamnatin jihar ta Kogi ta sa a gudanar da bincike kan wannan lamari kamar yadda Kwamshinan Lafiya na jihar Abdul-aziz Adeiza ya tabbatar, inda ya ce a yanzu haka an fara gwajin samfurin garin da suka ci domin yin tabbatar da ingancinsa.

Wannan na zuwa ne kasa da mako guda da wasu mutane uku ‘yan gida daya suka mutu a unguwar “Second Gate” na karamar hukumar Suleja a jihar Neja sakamakon suma sun ci wani rogo da suka saya a kasuwa suka dafa.

Sabbin Labarai
Labarai Masu Alaka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here