Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa Najeriya ba za ta taba yin nasara wurin cimma burinta ba matukar shugabanni da ‘yan kasa ba su rungumi abin da ya kira tsarin “mutunta juna” ba.
Obasanjo wanda ke magana a jiya Jumma’a, ya kuma yi gargadin cewa Najeriya na zaune a kan nakiya da ka iya fashewa idan har ta kasa daukar kwararan matakai da jajircewa wajen magance dimbin kalubalen da take fuskanta.
Ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai mataki biyu gaba, mataki daya a gefe, mataki hudu a baya. Ya kuma ce masu zanga-zangar neman kawo karshen gurbataccen Shugabanci na kan tsari, inda ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta saurari korafe-korafen jama’a, ta daina nuna cewa komai na tafiya daidai.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan majalisar wakilai guda shida, wadanda su ne masu daukar nauyin kudirin dokar neman mayar da wa’adin mulkin Shugaban Kasa zuwa shekara 6, da tsarin karba-karba a zaben shugaban kasa tsakanin Arewa da Kudu, da na kujerun gwamna dukkan jihohi 36.