Ana fargabar cewa Najeriya na iya fuskantar mummunar barkewar cutar kyandar biri (mpox) yayin da nahiyar Afirka ke fuskantar karuwar cutar da ba a taba ganin irinta ba tun farkon shekarar 2024.
Masana sun yi gargadin cewa wani sabon nau’in cutar ta kyandar biri na yaduwa ba tare da “an a kula ba” kuma ya na haifar da tsanani ga dubban mutane yayin da asibitoci ba su da isassun kayan aikin da za su iya dakatar da yaduwar.
Rahotanni sun nuna cewa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da makwabtanta na ci gaba da fama da barnar da cutar ta yi bayan barkewa a shekarar 2022 zuwa 2023, inda kusan mutane 100,000 suka kamu, lamarin da ya haifar da zazzabi mai tsanani tare da fetsuwar kiraje hade da kumburi a jikin mutanen.
Shekaru biyu kenan da hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana dokar ta-baci ta lafiya a duniya kan barkewar cutar ta “mpox”, cutar da ta bazu zuwa wasu kasashen duniya bayan barkewarya a nahiyar Afirka.