Hauwa Musa Abdullahi wadda aka fi sani da Hauwa Dana, ‘yar asalin jihar Neja ce daga karamar hukumar Shiroro.
Ta na daya daga cikin fitattun mata a Arewacin Najeriya da ke yin sana’ar da al’umma ta fi yadda da cewa maza ne kadai za su iya yi.

Duk da cewa ta yi karatu har ta kai ga matakin digiri, Hauwa ta sa kai tare da koyan sana’ar tukin motar noma wato “Tractor” a turance domin fadada hanyar samun abin biyan bukata kasancewar marainiya ce.

A zantawarta da Hausa Daily Times, matashiyar ta ce yau shekara 4 kenan da koyan wannan sana’a tun ta na karatu a jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida ta jihar Neja.
Baya ga wannan sana’ar, ta kuma ce ita kwararriya ce a aikin jarida.



A yanzu haka ita kadai ce mace a inda take aiki, kuma ta farko da fara wannan aiki na tukin motar nomaa matsayinta na mace da gwamnatin jihar kafin samun wasu da suka biyo bayanta a yanzu.