Daga Abdallah Yunus Abdallah
Ba zan yi magana a kan abin da ya jawo zanga zangar da aka yi ba, saboda dalilan a fili suke sai dai kowa da yadda yake kallon su. Amma nazarin da na yi a kan abubuwan da suka faru ne a zanga zangar.
In aka yi kyakkyawan nazari game da zanga zangar da aka yi musamman a Arewa, za ka gane akwai babban aiki a gaban gwamnati da iyaye. Saboda abubuwan da wasu matasan suka yi ya nuna tsabar rashin aikin yi da rashin tarbiyya da jahilci. Ban taɓa yarda cewa muna zaune a kan ‘time bomb’ ba ne sai yanzu. Akwai babban aiki a kan gwamnati. Amma dole in gwamnati ta motsa, iyaye ma fa sai sun yi nasu aikin.
Dadin abin an fara samun wasu daga cikin shugabannin Arewa, irinsu Sanata Uba Sani sun fito sun ce, dole duk wanda ya taba yin shugabanci a Arewa yana da hannu a cikin lalacewar Arewa saboda haka ya kamata su zo su zauna don magance matsalar da ke addabar yankin. Muna fata, Allah ya sa tsofaffi da shugabannin Arewa za su haɗu gaba ɗaya su hanyoyin da za a bi a magance matsalolin Arewa.

Akwai rashin aikin yi a Arewa da matsalolin tsaro wanda suka kara jefa yankin cikin tsananin talauci. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, wasu abubuwan da suka faru a wurin zanga zangar nan ya wuce maganar talauci, akwai matsalar rashin tarbiyya da kuma jahilci. Saboda babu wani Musulmi mai hankali, mai tarbiyya da zai shiga Masallaci da sunan zanga zanga ya sace duk abin da ke cikin masallacin har ya fasa ‘tiles’ ya kwashe a matsayin ganima.
A wasu wuraren an samu ɓata-gari sun fasa shaguna da runbunar ajiyar hatsi na bayin Allah sun kwashe. Sun fasa shagunan mutane, sun kwashe su. Sun kona motocin ‘yan uwansu talakawa. Lamarin dai akwai ban tsoro da tausayi. Saboda waɗannan matasan in ba a ɗauki mataki ba, babu wanda zai tsira a ƙasar nan; babu talaka babu mai kuɗi, babu mai muƙami, babu maras muƙami. Kuma ai hakan ya nuna, tunda ko a wannan zanga zangar ai ba su tantance wannan na wane ne. Sun ƙwace wayar talaka, sun ƙwace na masu hali. Hatta mai siyar da dabino wanda jalinsa bai wuce Naira dubu goma ba, ba su bar shi ba, sun sa masa wawa sun sace dabinon.
Abin takaci shi ne, wanda ya fito yana zanga zanga cewa ana zaluntarsa, ya kuma koma yana zaluntar/satar kayan ‘yan uwansa talakawa da sunan ganima. Lamarin sai an sake dubawa, gwamnati da shuganni su yi adalci su sauke haƙƙin da ke kansu, sannan kuma ni da kai mu ma mu gyara halayenmu, mu sauke nauyin da ke kanmu na tarbiyyan iyalanmu.
Allah ya zaunar da kasarmu lafiya da karuwan arziki.
Abdullah Yunus Abdullah,
Mai kishin Arewa da Najeriya.