Al’ummar mazabar Nasarawa ta Kudu a jihar Nasarawa, sun fara yekuwar yi wa dan Majalisar Dattijai mai wakiltan yankin Sanata Muhammad Ogoshi Onawo kiraye sakamakon zarginsa da suka yi da kasa tabuka musu komai tun bayan tafiyarsa majalisa.
Mutanen yankin wadanda suka fara gangamin yada bukatar, cikin wata takardar sanarwa da wani dan gwagwarmaya daga mazabar, Activist Shammasu Musa Dantsoho ya sanya wa hannu Hausa Daily Times ta samu kwafi, sun bayyana dalilin yin kirayen da kasa magance matsalolin da yankin ke fama da su da Sanatan ya yi, ta hanyar shigar da bukatar hakan a majalisa tare da nemo mafita.
Daga cikin matsalolin da suka bayyana, sun hada da fatara, yunwa, matsalar tsaro, karancin ababen more rayuwa, rashin aikin yi ga matasa da dai sauransu.
Sanata Muhammad Ogoshi dai fitaccen dan siyasa ne a jihar Nasarawa, wanda ya kasance dan majalisar dokokin jihar daga shekarar 2003 zuwa 2011, sannan ya zama dan majalisar wakilai daga shekarar 2011 zuwa 2019, kafin ya tafi majalisar dattijai a shekarar 2023 bayan ya yi takaran kujerar ta sanata ya fadi a zaben 2019 duk a karkashin jam’iyyar PDP.