Watanni biyu bayan ruftawar wata mahakar zinari a garin Galadiman Kogo na karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, an sake gano wasu gawarwakin mutane hudu daga ramin.
Lamarin wanda ya faru a ranar 3 ga watan Yunin 2024, ma’aikatan hakan zinari da dama ne mahakar ta rufta kansu, tare da makale da dama daga cikinsu.

Hakimin Galadima-Kogo, Malam Umar Aliyu, wanda ya tabbatar wa da manema labarai gano gawarwakin a ranar Laraba, Ya bayyana cewa tuni aka kai su dakin ajiye gawa na Asibitin kwararru na Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) da ke Minna.
Ya kara da cewa, biyu daga cikin gawakin wadanda suka mitun da yake musulmai ne, za a yi jana’izarsu a yau Juma’a a fadar Sarkin Minna.
“Sauran biyun kuma Kirista ne, za a mayar da su garuruwansu na Jihar Nasarawa kamar yadda iyalansu suka bukata”. A cewar Hakimin