Gwamnan jihar Edo ya rufe ofishin mataimakin gwamnan jihar Philip Shuaibu tare da hanashi shiga shi da ma’aikatansa.

A safiyar yau da mataimakin gwamnan ya je aiki ne ya tarar da kofar shiga ginin ofishin daure da sarka babu kowa wanda alamu ne da ke nuna cewa dagangan aka yi masa haka.

Jaridar Punch ta ruwaito Shuaibu ya tsaya a bakin kofar na wasu awanni kafin ya juya shi da hadimansa.

Mataimakin gwamnan wanda dama akwai jikakkiya tsakaninsa da gwamnan jihar Godwin Obaseki, ya ce babu wata takardar sanarwa ko umarni da ya samu na rufe ginin.