Monday, September 25, 2023
GidaDa Dumi-DumiTinubu ya nada tsohon Kwamishinansa gwamnan Babban Bankin Najeriya

Tinubu ya nada tsohon Kwamishinansa gwamnan Babban Bankin Najeriya

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Dattijai da sunan
Dr. Olayemi Michael Cardoso, tsohon Kwamishinansa a lokacin da yake gwamnan jihar Lagos, a matsayin sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya.

Yemi, wanda shi ne Kwamishinan Kasafi da tsare-tsaren tattalin arzikin jihar Lagos na farko, ya rike wannan mukami ne a shekarar 1999 bayan dawowar mulkin demokuradiyya Najeriya kuma a lokacin da Bola Tinubu ke gwamna.

Gogaggen ma’aikacin banki ne wanda ya yi aiki da manyan bankunan Najeriya da suka hada da Citibank,  Chase Bank da Citizens International Bank.

Haka zalika Shugaban ya kuma sake aikawa da sunayen mataimaka gwamnan Babban Bankin Najeriyan mutum hudu domin suma a tantancesu, ciki har da tsohon Kwamishinan Kasafi da tsare-tsaren jihar Kaduna a lokacin gwamnatin Malam Nasir Ahamd El-Rufa’i.

Ga sunayen kamar haka.

1. Uwargida Emem Nnana Usoro
2. Muhammad Sani Abdullahi Dattijo (tsohon Kwamishinan El-Rufa’i)
3. Philip Ikeazor
4. Dr. Bala M. Bello.

Isma'il Karatu Abdullahi
Isma'il Karatu Abdullahi
Isma'il Karatu gogaggen dan jarida ne da ya samu horo daga manyan kafafen yada labarai na duniya.
RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments