Khalifa, yaron da iyayensa suka jefar bisa zargin aljani ne shi ba mutum ba ya samu sabuwar uwa.
Mahaifiyarsa da kanta ta rinka muzgna masa tare da sauran ‘yan uwansa.

Bidiyonsa ya karade dandalin Tiktok a makon jiya, kuma mahaifiyarsa ce ta dauka an jiyota tana cewa ta gaji da rainon aljani ganin yadda yaki girma kullum sai kara kwajjamewa yake yi.

Ganin bidiyon ke da wuya fitacciyar matashiyar ‘yar kasuwar nan Hajiya Layla Ali Othman ta sa a nemo mata shi tare da alkawarin rikeshi domin samun kulawa.

Bincike ya gano yaron rashin kulawa ne da cin abinci mai gina jiki suka yi tasiri ga lafiyarsa.






Tuni dai wadda ta yi jagoranci wurin naima wa Khalifa taimako wato tsohuwar Jarumar Kannywood Mansura Isah ta mikashi ga ita Layla a Abuja tare da rakiyar mahaifiyarsa wadda ta yi nadamar abin da ta aikata.