Tuesday, September 26, 2023
GidaKunnen GariNi matar aure ce kuma da izinin mijina nake fim- Jaruma Fatima...

Ni matar aure ce kuma da izinin mijina nake fim- Jaruma Fatima na cikin shirin Fatake

Jaruma Amina Umar wadda aka fi sani da Fatima a cikin wani sabon shiri mai dogon zango Fatake ta bayyana cewa ita matar aure ce har ma tana da yara.

Jaruma Amina Umar (Fatima) a cikin shirin Fatake

Amina wadda ta bada takaitaccen tarihinta a yayin hira da tashar Freedom Radio Kano, ta ce ita haifaffiyar kasar Ghana ce amma iyayenta ‘yan asalin kasar Nijar ne.

Mijin jarumar da ‘ya’yanta biyu.

Ta ce tun a shekarar 2011 ta yi aure kuma Allah ya albarkacesu da ‘ya’ya biyu. 

Kasancewa abu ne mai matukar wuya samun mace mai aure a masana’antar Kannywood ta Najeriya, Amina, ta ce da izinin mijinta take wannan sana’a hasali ma, shi ya rinka bata kwarin gwiwa tun kafin sana’ar ta shiga jikinta.

Jarumar da abokan aikinta ciki har da Jarumi Sadik Sani Sadiq a bakin aiki a Nijar.

Da aka tambayeta yanda ta tsinci kanta cikin harkar fim, jarumar ta ce an je daukan shirin Fatake a kasar Ghana ne ta samu damar neman shiga cikin shirin bayan yin gwaji kuma sai Allah ya bata nasara.

Jarumar da mijinta.

A yanzu dai, ta ce karfin aikin ya dawo Najeriya, hakan ke sa lokaci zuwa lokaci takan bar iyalinta a Ghana zuwa Kano ko duk inda aiki a Najeriya kuma hakan bai canza komai tsakaninta da mijinta ba.

Wannan dai abu ne mai wahala samun mace jaruma wadde take da aure a masana’antar shirya fina-finan Hausa, wasu ma na ganin baya ga haramci a addini hakan ya saba al’adun Malam Bahaushe a Arewa.

Isma'il Karatu Abdullahi
Isma'il Karatu Abdullahi
Isma'il Karatu gogaggen dan jarida ne da ya samu horo daga manyan kafafen yada labarai na duniya.
RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments