Majalisar dokokin jihar Kebbi ta nuna goyon baya tare da amincewa da salon jagorancin gwamnan jihar Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) sakamkon irin nasarorin da ya samu cikin kwanaki 100 da hawansa kan karagar mulki.
Majalisar ta tabbatar bayyana hakan ne biyo bayan kudirin da aka gabatar a gabanta kuma dukkan ‘yan majalisar suka amince yayin zamanta a ranar Alhamis.

‘Yan majalisar sun nuna kwarin gwiwarsu akan gwamnan ganin yadda a cewarsu kwanaki dari ya dora jihar bisa turbar ci gaba musamman a fannin ilimi, lafiya, yaki da matsalar tsaro tare da samar da bababen more rayuwa.
Shugaban Majalisar Muhammad Usman Zuru ya kira ga sauran masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati da su yi koyi da gwamnan ta hanyar maida hankali wurin gudanar da aikinsu yanda ya dace.