Tuesday, September 26, 2023
GidaKunnen GariAbba ya manta da mu bayan akansa aurena ya mutu - cewar...

Abba ya manta da mu bayan akansa aurena ya mutu – cewar wata ‘yar Kwankwasiyya

Wata bazawara ta nemi gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ya waiwayesu duba da irin gudumawar da suka bayar na samun nasararsa, a sakamakon haka har aurenta ya mutu.

Matar mai suna Hauwa Abdullahi da aka fi sani da Hauwa Fulani, ta bayyana haka ne a hirarta da gidan radiyin Freedom Kano.

Hauwa Fulani

Ta ce ita ‘yar tafiyar Kwankwasiyya ce daga tsagin kungiyar Kwankwasiyya Tiktokers, tun kafin shekarar 2019 suke tafiyar Kwankwasiyya har yanzu da aka kafa gwamnati amma ba su fara ganin alamar za a tafi da su ba.

Ta ce a ta dalilin tafiyar Kwankwasiyya, har saba umarnin mijinta ta yi kasancewar ba jam’iyyarsu daya ba, haka ya kai ga rabuwan aurenta da shi ya kuma yi mata korar kare daga gidansa.

Da take zayyana irin gudumawar da ta baiwa tafiyar gwamna Abba, Hauwa ta ce; “da ni aka zagaya kananan hukumomin Kano 44 wurin kamfe, sannan ina daga cikin ‘yan gaba-gaba wurin wayar wa da mata kai a lokacin yakin neman zaben Abba Gida-gida. Tun mata ba su san shi ba nake buga fastoci da kudina ina binsu gida-gida ina fada musu wanda za su zaba ranar zabe”.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments