Thursday, September 21, 2023
GidaKunnen GariMatashi ya auri mata 7 rana daya a kasar Uganda

Matashi ya auri mata 7 rana daya a kasar Uganda

Wani dan kasuwa dan kasar Uganda, Habib Nsikonnene, ya auri mata bakwai a rana daya.

An yi bikin auren ne a ranar Lahadin da ta gabata 10 ga watan Satumban 2023 a kasar.

Shafin tashar Capital FM na kasar ne ya bayyana haka a dandalin sada zumunta na X wato Twitter.

An bayyana sunayen matan da: Mariam, Madina, Aisha, Zainabu, Fatuma, Rashida, sai Musanyusa, wadda aka bayyana a matsayin matarsa ta farko da suka shafe tsawon shekaru 7 suna tare.

Sai dai an gano biyu daga cikin matan ‘yan gida guda ne kuma uwa daya uba daya.

Bayan daurin auren, an gonya gwangwaje kowanne daga cikinsu da sabuwar motar alfarma, kowanne dauke da sunanta a jiki.

A jawabinsa a wurin liyafar bikin, Habib ya yaba da biyayyar matar a gareshi, sannanya ce, “matana babu kishi a tsakaninau. Na yanke hukuncin aurensu rana daya ne domin samar mana da farin ciki a matsayin iyali daya. Sannan, kasancewar har yanzu ina da sauran kuruciya, nan gaba kadan zan iya kara auren wasu”.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments