Wani jami’in dan sanda ya bindige wani yaro dan shekara 12 mai suna Sani Danlami da kakarsa a wurin rabon tallafin abinci (palliative) a karamar hukumar Rijau na jihar Neja.
Wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi sakamkon rikici da ya kaure wurin rabon abincin a cikin garin Rijau.
Hausa Daily Times ta gano cewa dan sandan ya yi harbi ne saman iska domin tarwatsa taron masu rikicin, sai tsautsayi ya gifta kan wannan yaro da kakarsa harsashi ya samesu a hannayensu na dama akan hanyarsu ta zuwa wurin rabon.
Bayanai sun ce, yaron da kakarsa ‘yan gudun hijirane da matsalar tsaro ta rabasu da garinsu zuwa neman mafaka a Rijau.
An yi nasarar ceto rayuwarsu a asibiti mafi kusa da inda tsautsayin ya auku, sai dai daga bisani an garzaya da yaron zuwa babban asibitin kwararru dake Minna bisa mummunar rauni da ya samu.

Babban Kwamishinan Lafiya na jihar Dr. Tukur Bello wanda kuma shi ne shugaban kwamitin raba tallafin abinci na karamar hukumar ta Rijau, ya ce abin da ya faru tsautsayi ne, sannanya tabbatar da cewa yaron yana samun kulawa.