Tuesday, September 26, 2023
GidaKunnen GariMutum 30 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Neja

Mutum 30 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Neja

Rahotanni daga jihar Neja na cewa akalla mutame 30 ne suka rasa rayukansu a sakamakon hatsatin kwale-kwale da ya rutsa da manoma a kan hanyarsu ta zuwa gona, wadanda suka fito daga kauyukan Gbajibo, Ekwa da Yankyade a karamar hukumar Mokwa a jiya Lahadi.

Wani mazaunin daya daga cikin kauyulan da wadanda jirgin ya rutsa da suka fito ya shaida wa Hausa Daily Times cewa wani kututturen itace ne jirgin ya buga bai sani ba, wanda hakan ya sa jirgin ya rabe a tsakiyar ruwan.

Kaburburan wasu daga cikin wadanda suka mutu a ruwan.

Mutumin mai suna Musa Byagi, ya ce akwai ‘yan uwa da makotansa a cikin jirgin.

Shugaban Hukaumar Agajin Gaggawa na jihar Garba Salihu ya tabbatar wa da wakilinmu mutuwar mutane 30 wadanda aka tsamo gawakinsu daga ruwa, yayin da ya ce an ceto wasu karin mutane 30.

Ya yi karin haske da cewa duk da babu tabbacin adadin mutanen da ke cikin jirgin yayin da hatsarin ya auku, Garba ya ce wadanda aka ceto sun bayyana cewa sama da mutum dari ne ke cikin jirgin.

A halin yanzu dai ya ce jami’ansu masu ceto da hadin gwiwar Sarkin Ruwa da matasan yankin na ci gaba da lalube ko za a gano sauran gawakin da suka bata.

Kaburburan wasu daga cikin wadanda suka mutun.

Jihar Neja dai ta yi fama da yawan hatsarin kwale-kwale a ‘yan shekarun nan, wanda ake ganin wannan shi ne kusan na biyar a cikin shekaru biyu.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments