Wani magidanci a birnin Kano, ya tashi hankalinsa tare da yin gaggawar kai kara kotu sakamakon ikirarin da matarsa ta yi na sake yi masa kaciya.
Magidancin mai suna Malam Ali, ya tinkari kotun shari’ar musulunci da ke Rijiyar Lemo ne domin neman a dakatar da matarsa daga wannan alwashi da ya yi.
Ya shaida wa kotun cewa mai dakin nasa ta jima tana faɗa ma sa cewa za ta sabunta masa kaciya, tare da tabbatar wa da alkalin kotun cewa a yanzu haka ma ta sayo wuƙa mai kaifi don cika aiki.
- Sojoji sun gano inda ake kera bindigogi a Kaduna
- Ba mu yadda da hukuncin kotu ba, za mu daukaka kara- Abba Kabir Yusuf
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, dama mijin mata biyu yake da su, ya ce tun ranar da ta yi wannan iƙirarin ya daina bacci da ido biyu a duk ranar kwananta.
Ya bayyana cewa, a yanzu haka ya yi nasarar dauke wukar daga dakinta, sai dai har yanzu a firgice yake domin bai san mai zai iya faruwa zuwa gaba ba.