Wani saurayi a jihar Kano ya yaudari budurwarsa da suka shafe shekara takwas suna soyayya, aka daura masa aure da wata ba tare da ta sani ba. Hatta kayan lefen auren wadda ya aura ita ce ta hada da sunan nata ne ba tare da ta sani ba.
Budurwar mai suna Maryam Nuruddeen Shuwa, mazauniya unguwar Gwammmaja ce da ke karamar hukumar Dala a tsakiyar birnin Kano, ta bayyana abin da saurayin ya yi mata ne a cikin shirin Yankan Kauna da tashar Dala FM ke yi a shafinsu na Facebook.

Ta ce shi ne saurayinta na farko tun tana ‘yar JSS 3 a karamar makarantar Sakandare suie tare, har maganar aure ta shiga tsakaninsu ya tura iyayenshi domin ganawa da iyayenta.
Kwatsam wata rana sai ta ci karo da katin gayyatar aurensa a dandalin sada zumunta har da ma wakar bikin auren. “Sai na tuntubi babban abokinsa wanda ya tabbatar min da hakan, amma shima ya yi mamakin yadda ne ce masa ban san da labarin auren ba”.

“Daga nan sai na tura masa (saurayin da ya yaudareta din kenan) a WhatsApp katin aure da ma wakar bikinsu, shima ya yi mamakin inda na samu har yake tambayana ina na samu, daga karshe yake fada min cewa na kwantar da hankalina, har yake cewa wannan ba zai sa ya kasa aurena ba”. A cewar Maryam.

Budurwar ta ci gaba da bayyana cewa abin da ya fi ci mata rai kuma ba za ta taba mantawa ba shi ne yadda ya yaudare ta da hada kayan lefen da ya ce nata ne, alhali na nata bane na wadda ya aura ne domin a lokacin da take hadawa idan ya tura mata da kudi ta saya kayan shi take turawa kayan ya ajiye a wurinshi.
Wannan lamari dai a cewarta ya kaita ga kwanciya rashin lafiya duk da kokarin da ta yi na karfafa zuciyarta ta yanda ba zai dameta ba.

Yanzu dai ta ce komai ya wuce duk da hakan na da matukar wahala, dominta ci gaba da harkokinta na kasuwanci tare da barwa Allah komai. Har iyayenta fatan Allah ya sa haka shi ya fi zama alkhairi suka mata domin basu dauki matakin tuntubar iyayensa ba a cewarta.
Sai dai Maryam ta ce zuciyarta ta kasa yadda da wani namiji da sunan soyayya domin gani take yi kamar sake yaudararta za a yi.