Thursday, September 21, 2023
GidaDa Dumi-DumiGwamnatin jihar Kebbi ta baiwa ɗan Sheikh Giro muƙami

Gwamnatin jihar Kebbi ta baiwa ɗan Sheikh Giro muƙami

Kwnaki bayan rasuwar Sheikh Abubakar Abdullahi Giro Argungu, gwamnan Kebbi Nasiru Idris ya maye gurbin marigayin da dansa a matsayin mamba a Hukumar Jindadin Alhazai na jihar.

Shekaru da dama kenan marigayin na rike da wannan matsayi, wanda shi ke jagorantar bitar Alhazai a kasa mai tsarki a duk lokacin aikin Hajji.

Nadin Sheikh Hussaini Abubakar Giro dai ya biyo bayan kira da Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abubakar Bala Lau ya yi wa gwamnan jihar da ya maye gurbin marigayin da daya daga cikin ‘ya’yansa kuma ya amince da hakan, a cewar sanarwar nadin da Sakataren Yada Labarun gwamnan Ahmed Idris ya fitar.

Sheikh Hussaini shima mahaddacin Al-Qur’ani ne, sannan ya yi karatu mai zurfi kama daga na bokon zuwa na addini wanda kuma yana daya daga cikin mayan matasan Malamai masu tasowa.

Idan baku manta ba a ranar Laraba da ta gabata 6 ga watan Satumba ne Allah ya yi wa Sheikh Giro Argungu rasuwa bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya a asibitin tunawa da Sarki Yahaya da ke Birnin Kebbi fadar jihar, kuma aka yi masa sutura washegari Alhamis a mahaifarsa ta Argungu.

RELATED ARTICLES

1 comment

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments