Thursday, September 21, 2023
GidaJi Ka KaruAbin da mai tukin mota zai yi idan tayarsa ta fashe yana...

Abin da mai tukin mota zai yi idan tayarsa ta fashe yana tsaka da tafiya

A lokuta da dama abin da ke zuwa zukatan mafi yawan matuka idan suna tsaka da tafiya tayar motarsu ta fashe shi ne su taka birki nan take sakamkon razana da suke yi. Yana da kyau ku sani hakan na da matukar hadari.

A sabili da haka, ku sabar da zukatanku natsuwa a irin wannan yanayi, sannan ku yi kokarin bin wadannan matakai za su amfanar da ku matuka;

Idan kuna tsaka da tafiya tayar motarku ta fashe, ma’ana ta yi bindiga, ga abin da za ku yi.

1. Na farko, kar a taka birki nan take; motar za ta iya juyawa ta yi ta dungurawa in har aka kuskura aka taka birki a irin wannan yanayi.

2. Na biyu, Ka taba alamar fitilar da ke nuna motarka na cikin damuwa “Harzard Light”

3. Na uku, direba ya dage kafarsa daga kan totur a hankali ba lokaci daya ba.

4. Na hudu, karike sitarinka da kyau kuma ka nufi gabanka kar ka juya sitarin ko wani gefe. Katabbatar ka rike shi gam.

5. Na biyar, kabar motar ta tsaya a sannu a hankali; kar ka taka birki fa!

Idan Allah ya sa duk wani mai tuki ya tsinci kansa cikin wannan yanayi kuma ya bi wadannan matakan, komai zai zo da sauki.

Allah ya karemu.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments