Fitaccen mawakin nan mazaunin Amurka Akon ya shawarci mutane da su kasance marowata, ma’ana su tsuke bakin aljuhunansu in har suna son su tabbata masu kudi.
Mawakin wanda ke daya daga cikin hamshakan mawaka a Afrika ya bayyana haka ne a wani hira da aka yi da shi a kwanan nan a kafar Impaulsive, inda ya yi wa kansa lakabi da marowaci.
Ya ce, “Idan kana son zama mai arziki, ka kasance marowaci. Idan kana neman mutumin da ya fi kowa rowa a duniya in ka sameni ka gama”
Akon ya kuma gargadi fitattun mawaka ‘yan uwansa da ma masu tasowa da su guji mallakar jiragen sama na hawa domin a cewarsa, suna da wuyan sha’ani a bangaren kula.
“Na yi ƙoƙarin mallakar jirgin sama, amma ko da na saya watanni 6 kawai na yi da shi na sayar babu shiri. Idan dai bukatar dole ta taso na zuwa wani wuri da shi ina zuwa na dauki na haya, nan din ma sai mun daidaita da masu shi, don haka ku ma wannan ya zama wani ɓangare na dabarun ku na tattakin kuɗi. Amma ina baku shawarar duk abin da kuke yi, kada ku mallaki jirgin saman hawa.
“Mallakar jirgin sama yana nufin duk shekara sai ka kashe dala miliyan biyu zuwa uku don kawai kula da shi. Kudin da ake kashewa na kula da jirgi ya fi ainihin kudin da aka sayeshi.