Wani matashi dan kasar Japan mai suna Toco ya cika babban burinsa na zama kare.
Wannan mutumin ya kashe dala 14,000 (kwatankwacin naira miliyan 12) don a canza masa suffa zuwa ta kare, aikinda wani kamfanin kasar Japan ya masa.

Bayanai sun ce a baya yana faki idon mutane ya bayyana akan tituna ba tare da an san shi ne ba, amma daga ƙarshe ya yanke shawarar bayyana wa duniya sabuwar suffarsa a karon farko a matsayin kare.
Idan ya sa aka yi masa bidiyo ya dora a kafafen sada zumunta domin burge mabiyansa, akai-akai Toco na aiwatar da ayyuka daban-daban irin na kare kamar tafiya yawo, shiga cikin keji, shan coke da dai sauransu.

Hakan ya bayyana yadda matashin ke jin dadin sabuwar rayuwar da ya sayan ma kansa.
A kwanan nan an gan shi yana tafiya a fili a matsayin kare. Wani abin mamaki, har abokai yake yi da karnukan da ya hadu da su idan ya fita. Da yawa masu wucewa a hanya sun gamsu da haƙiƙanin bayyanar Toco a matsayin kare. Kama daga haushinsa da salon tafiyarsa tamkar na kare.

A zahiri idan ba a fada wa mutum ba,ba wanda zai gane cewa shi mutum ne ba karen gaskiya ba.

Toco ya bayyana cewa tun yana yaro yake da burin zama kaman kare. Sai dai yana gudun abin da mutane za su ce idan ya canza suffarsa zuwa karen.