A wayewar garin yau Juma’a mutanen unguwa suka tsinci gawar wani matashi a daidai wani transifoman rarraba wuta dake yankin Printing Press bayan tsohuwar Sakateriya da ke Minna fadar jihar.
Birnin Minna da wasu kananan hukumomin jihar irinsu Lapai, Suleja da dai sauransu na fama da matsalar barayin transifoma wadanda ke fakan idon mutane su sace wayoyi masu amfanu daga jikin tiransifomomin unguwanni.
An sha kama irin wadannan batagari amma kuma babu wani kwakwaran hukuncin da ake yanke musu, galibima basu kwashe makonni a tsare za a gansu cikin al’umma.