Monday, September 25, 2023
GidaLabarun KetareTa ina musulmai za su kara aure tunda kun tauyesu- Martanin wani...

Ta ina musulmai za su kara aure tunda kun tauyesu- Martanin wani dan siyasa ga gwamnatin India

Yayin da gwamnatin jihar Assam ke shirin haramta auren mata fiye da daya a jihar, Badruddin Ajmal, shugaban kungiyar All India United Democratic Front ya ce dama musulmai sun yarda da auren mace daya, tun can mabiya addinin Hindu ne aka fi sani da auren mata barkatai.

Ajmal ya fadawa manema labarai a ranar Juma’a cewa, ” Babban Ministan Assam ya kwace komai daga hannun musulmai mazauna jihar. Ya hanasu aikin yi ko sana’a, dan kasuwancin sayar da kayan lambu da suka koma dogaro da shi ya sake hanasu. Ko musulmi na son kara aure ma bai da hali yanzu.

Hon. Ajmalwanda shi ne dan majalisa mai wakiltar yankin Dhubri Lok Sabha a jihar ta Assam, ya ci gaba da cewa a zamanin yau mabiya addinin Hindu ne ke auren mata da yawa a India.

Tun da farko, Babban Ministan Assam, Himanta Biswa Sarma, ya tabbatar da cewa akwai gagarumin goyon bayan jama’a kan matakin da gwamnatinsa ke so dauka na haramta auren mace fiye da daya a jihar.

Gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti don nazarin yiwuwar gabatar da dokar hana auren mata fiye da daya a Assam. Bayan gabatar da rahoton kwamitin da abin ya shafa, gwamnati ta nemi ra’ayin jama’a kafin a kawo wata doka a majalisar dokokin jihar.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments