Thursday, September 21, 2023
GidaKunnen GariHamshakin matashin attajirin Birtaniya Alfie Best Jr ya musulunta

Hamshakin matashin attajirin Birtaniya Alfie Best Jr ya musulunta

Daya daga cikin hamshakan matasan ’yan kasuwa da suka yi fice a Burtaniya, Alfred William Best, wanda aka fi sani da Alfie Best Jr, ya musulunta.

A ‘yan watannin da suka gabata, Alfie ya wallafa wani hotonsa cikin masallaci tare da rubuta cewa, “Idan Allah ya shiryar da mutum, babu mai iya ɓatar da shi. Hakazalika idan kuma ya ɓatar, to, babu mai shiryarwa.

Kwanan nan kuma, ya sake wallafa wani bidiyon kansa tare da rubuta cewa, “Dukkan godiya ta tabbata ga Allah… Alhamdulillah.”

Alfie dai ɗa ne ga hamshakin attajirin nan gidan shakatawa na ‘mobile’ park London wato Alfie Best Sr. Alfie Jr , mai shekaru 25, mahaifinsa ya mallaki kuɗi da ya kai kimanin fam miliyan 700, a cewar shafin jaridar Sunday Times ta Rich List.

An haifi matashin dai a shekarar 1997 a London kuma ya gaji sana’ar mahaifinsa wanda a yanzu haka shima ya mallaki manyan wuraren shakatawa a Birtaniya.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments