Tuesday, September 26, 2023
GidaLabarun KetareAn sake juyin mulki a Gabon, kasar da ke karkashin ikon uba...

An sake juyin mulki a Gabon, kasar da ke karkashin ikon uba da ɗa tsawon shekaru 56

Wasu gungun manyan hafsoshin sojin Gabon sun bayyana kigar da gwamnatin Ali Bongo a gidan talabijin na kasar, suna masu ikirarin cewa babban zaben kasar da aka gudanar a baya-bayan nan na cike da magudi.

A dalilin hakan, sun sanar da soke sakamakon zaben tare da rufe dukkan kan iyakokin kasar har sai in ma sha Allah.

Shugaba Ali Bongo ya sake lashe zaben shugaban kasa karo na uku da kashi 64.27% na kuri’un da aka kada, a cewar cibiyar zaben kasar a yau Laraba, bayan da aka samu jinkirin gudanar da zaben wanda ‘yan adawa suka ki aminta da shi bisa zargin tafka magudi.

Da yake sanar da sakamakon zaben da sanyin safiyar yau, shugaban hukumar zaben, Michel Stephane Bonda, ya ce babban abokin hamayyar Bongo, Albert Ondo Ossa, ya zo na biyu da kashi 30.77%. Yayain da tawagar Bongo ta yi watsi da zargin da Ondo Ossa ya yi na tafka magudi a zaben.

Kasar Gabon dai ta kasance karkashin mulkin uba da da tun daga shekarar 1967. Omar Bongo (wato baban Ali Bongo) ya kasance a kan karagar mulkin kasar tun daga shekarar alif 967 har zuwa mutuwarsa a shekarar 2009, daga nan ne ɗansa Ali Bongo ya gajeshi shima har zuwa yanzu da aka kifar da gwamnatinsa.

Kafin Ali Bongo ya zama Shugaban kasa, Shi ne ministan harkokin wajen Gabon a gwwmnatin baban daga 1989 zuwa 1991, daga bisani ya zama dan majalisar tarayyar kasar ya wakilci mazabar Bongoville kuma a matsayin mataimakin Shugaban Majalisar daga 1991 har zuwa 1999. Barinshi majalisar ne baban ya nada shi ministan tsaron daga 1999 har zuwa 2009 da uban ya rasu ya gaji kujerar shugabancin Gabon.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments