Tuesday, September 26, 2023
GidaKunnen GariKo kun san adadin al'ummar musulmi a Faransa da tasirinsu?

Ko kun san adadin al’ummar musulmi a Faransa da tasirinsu?

Sakamakon wani bincike da aka yi tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020 ya nuna cewa kashi 10 cikin dari na al’ummar kasar Faransa ne kawai musulmi.

A cewar hukumar kididdiga ta Insee da ta gudanar binciken, baya ga kaso 10 da ke wakiltar musulumi, kaso 29 ya nuna cewa kiristoci ne (Catholic) yayin da sauran addinai suka samu 10, marasa addini ‘yan ba ruwana kuma suka zama mafi rinjaye da kashi 51.

A cewar rahoton binciken, bakin haure da suka fito daga kasashen musulmi ne suka fi tsunduma cikin harkokin addini, yayin da wadanda suka fito daga Turai, ban da kasar Portugal, ko kasashen Asiya, ke ikirarin cewa ba su da alaka da addini.

Sai dai “kashi 20% na musulman dake kasar ne kawai ke zuwa masallatai akai-akai,” in ji Insee.

Rahoton ya kara da cewa kashi 75% na musulmai a kasar suna azumi da sauran ibadun addinin sosai yayin da kashi 15% na nuna halin ko-oho akai.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments