Tuesday, September 26, 2023
GidaKunnen GariAtiku, Kwankwaso da Obi na duba yiwuwar dunkulewa wuri daya

Atiku, Kwankwaso da Obi na duba yiwuwar dunkulewa wuri daya

A ci gaba da shirye-shiryen tarbar hukuncin kotun karbar korafe-korafen zabe, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, da Peter Obi sun fara wata tattaunawa na duba yiwuwar hadewa wuri daya da manufar kafa jam’iyyar da za ta fi kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Jaridar This Day ta ruwaito an gano fara tattaunawar wadannan ‘yan siyasa uku ne tsakanin Atiku da Kwankwaso, kafin daga bisani su amince Peter Obi ya shigo cikinsu. Dukkaninsu dai idan ba a manta ba sun tsaya takarar kujerar Shugaban Kasa a Jam’iyyun PDP, NNPP da LP a zaben 2023.

Tattaunawar wadda aka ce har yanzu tana kan matakin farko, an kafata ne kan ginshiƙai biyu. Na farko, a cewar ‘yan cikin gida, shugabannin uku sun yanke shawarar jiran sakamakon koke-koken zabe da ke gaban kotu, wanda zai tabbatar da ginshikin tattaunawar na biyu.

Misali, wasu majiyoyi sun yi nuni da cewa shugabannin suna sa ran cewa kotun za ta yi hukunci bisa “adalci” don tabbatar da cewa zaben da ya bai wa Shugaba Bola Tinubu nasarar kaiwa ga karagar mulki ba sahihi bane, hakan zai sa ta yi abin da ya dace. Dangane da haka ne aka ce Atiku, Kwankwaso da Obi suke fatan cewa kotun za ta rushe zaben ko kuma yin kira da a sake yin zagaye na biyu, wanda hakan zai sa su dunkule wuri daya domin su kalubalanci Tinubu da APC.

Sai dai idan kotun ta yanke hukuncin akasin haka, an ce shugabannin na tunanin kafa wata babbar jam’iyya gabanin zaben 2027, domin shirya karbar ragamar mulki daga hannun jam’iyyar APC.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments