Akalla dakarun soji 21 ne suka mutu ciki har da manyan hafsoshi tare da raunata wasu ‘yan banga biyar a yayin wani gumurzu da da suka yi da ‘yan bindiga a garin Kundu da ke kusa da Zungerun a karamar hukumar Wushishi ta jihar Neja.
Rahotanni sun ce lamarin ya fara afku ne a ranar Lahadi, inda ‘yan bindigan suka kashe goma sha uku daga cikinsu sojojin a arangamar da suka yi da yayin da aka kashe wasu sojoji takwas a yau wani harin kwantan bauna, cikin wadanda aka kashe har da manyan sojin masu matsayin Kaftin da Manjo.
Wata majiya da ta nemi a saka sunanta ta shaida wa Hausa Daily Times cewa lamarin ya faru ne a lokacin da jami’an tsaron na kokarin tare hanyar da ‘yan ta’addan za su wuce bayan sun sato shanu da dama.
Majiyar ta kara da cewa, a asibitin Zungeru aka jibge gawarwakin sojojin ashirin da daya da aka kashe, kafin jirgin sojin saman Najeriya ya kwashesu zuwa Kaduna wanda shima daga bisani ya yi hatsari a wani kauye a karamar hukumar Shiroro duka a yau.
‘Yan banga biyar da suka samu raunukan harbn bindiga tare da sauran sojin da suma suka jikkata na karban magani a asibitoci daban-daban.
Har izuwa yanzu babu sanarwa daga rundinar Sojin Najeriya ko gwamnatin jihar Neja a hukumance dangane da wannan hari, sai dai rundinar sojin saman Najeriya ta tabbatar da afkuwar hatsarin jirgin samanta.