Monday, September 25, 2023
GidaDa Dumi-DumiWata kurtun soja ta harbe kyaftin har lahira a jihar Adamawa

Wata kurtun soja ta harbe kyaftin har lahira a jihar Adamawa

Wata macen soja yayin aikin aiwatar da dokar hana fita da gwamnatin jihar Adamawa ta sanya ta harbe wani abokin aikinta da ke gaba da ita a matsayi a daidai shingen bincike da ke mashigar Jimeta, babban birnin jihar.

In ba a manta ba a makon jiya gwamnan jihar Ahmadu Fintiri ya sanya dokar ta-baci bayan da aka samu bata-gari da suka fasa ma’ajin gwamnati tare da wawashe kayan abinci da aka tanada domin rabawa a matsayin tallafi don rage radadin cire tallafin man fetur.

Sai dai a yayin aiwatar da dokar a kan hanya, sojar da wadda aka bayyana sunanta da Lance Corporal Nkiru ta harbe ogan nata mai mukamin kyaftin da ya yi kokarin shiga tsakani a rikicinta da fararen hula.

Shaidun gani da ido sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa ma’aikaciyar ta dage cewa masu ababen hawa da ke dawowa gida a lokacin dokar ta-bacin ala-tilas sai dai su koma inda sukafito.

An ce an yi kokarin garzayawa da mamacin zuwa FMC Yola, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Tuni dai aka kama wadda ta aikata ta’asar tare da tsareta.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments