Thursday, September 21, 2023
GidaSiyasaGanduje ya bayyana dalilin cire sunan Maryam Shetty

Ganduje ya bayyana dalilin cire sunan Maryam Shetty

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Abdullahi Umar Ganduje, ya magantu kan cire sunan fitacciyar ‘yar soshiyal mediyar nan Dr. Maryam Shetty wadda sunanta ya kasance daga cikin wadanda aka nada mukamin Minista a sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Ganduje, yayin hira da ‘yan jarida a Abuja, ya ce ba da yawunsa aka sanya sunanta ba,sannanbai da hannu wurin cire sunan, kawai shawarasa shugabankasa ya nema kafin a cire sunanta bisa cece-kuce da hakan ya haifar.

Maryam Shetty rusune gaban Shugaba Bola Tinubu yayin yakin neman zaben 2023.



Ya bayyana dalilai uku na cire sunan Shetty da cewa, “mutanen soshiyal media sun soki nadin da aka yi mata, wanda har haka ya kai ga wasu na cewa al’ummar Kano sun rasa wacce za ta wakilcesu sai wannan”.

Ya ci gaba da cewa, “Wannan lamari ya haifar da damuwa sossai, donhaka da aka ja hankalin Shugaban kasa game da sunanta, sai ya tambayeni ko inda da masaniya game da sunata lokacin da aka bayar sai na ce masa ni ban san komai ba, a nan ne ya tambaye ni ko akwai bukatar a canza, nikuwa na ce kwarai da gaske,domin mulki irin wannan na bukatar kwarewa, dattako tare da sanin irin rawa da mutum ya taka wurin kafa gwamnati” a cewar Ganduje.

Daga karshe ya tabbatar da cewa Maryam ta bada gudunmawa daidai gwargwado wurin samun nasara APC a zaben da ya gudana amma wannan kujera ta Minista ya fi karfinta. Inda ya bayyana cewa ba za a barta haka kawai ba domin za a bata mukami amma daidai da ita.

Ita ma a sakon da ta wallafa a shafinta na Fasbuk jim kadan bayan samun sanarwar Shugaba Bola Tinubu ya janye sunata a ranar Juma’a bayan ta isa majalisar dattijai inda za a tantanceta.

Maryam Shetty ta bayyana cewa ta karbi matakin da Shugaban kasa da ma jam’iyyarta ta APC ta dauka akanta, wadda ta kara da jaddada cewa ba za ta gajiya ba wurin ci gaba da yin biyayya ga jam’iyyar tare da bada goyon bayanta kamar yadda ta saba.

Ta kuma yi godiya ga Tinubu bisa matakin da ya fara dauka na bata mukamin minista. 

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments