Monday, September 25, 2023
GidaKunnen GariDalilin da ya sa na ki bacewa lokacin da aka zo yin...

Dalilin da ya sa na ki bacewa lokacin da aka zo yin garkuwa da ni- Boka

Shahararren bokan nan da aka yi garkuwa da shi a makon jiya a jihar Anambra, Chidozie Nwangwu, wanda aka fi sani da “Akwa Okuko Tiwaraki”, ya ce da gangan ya ki amfani da laya domin bacewa lokacin da aka zo garkuwa da shi.

An yi garkuwa da Mista Nwangwu ne a Triple P Hotel da ke garin Oba a karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar.

Sai dai an sake shi a ranar Asabar, mako guda da sace shi.

Sai dai da yake ba da labarin abin da ya faru da shi, bokan ya ce yana da abin da zai hana a sace shi amma bai yi amfani da shi ba ya mika kansa ga wadanda suka yi garkuwa da shin gudun kada a kashe shi kamar yanda suka kashe masu tsaronsa biyu.

Ya ce, “Ainihin abin da ya faru shi ne, a gida a ranar, da misalin karfe 11:30 na safe, sai wani ya kira ni ya ce suna otal dina suna sharholiya da kudi domin sun kashe kusan Naira 300,000, za su so na je na samesu a wataya da ni.“Nan take na amsa gayyatarsu na ce su jirani gani zuwa, ni kuwa na nufi otal din ni kaɗai, a cikin sabuwar motata. Bai wuce mintuna 30 da isa na wurin ba sai na fara jin karan harbin bindiga yana tashi a iska. Mutane suka fara gudu. Ni kuwa na fita waje domin na ga me ke faruwa, sai mutanen suka fara harbina.

“Sun kashe jami’an tsaro na biyu. Ba na so in tsawaita magana a yanzu, amma na san cewa abubuwa biyu ne kawai za su iya ceton tseratar da mutum a wannan yanayi. Idan laya ba ta cece ka ba, kuɗinka zai cece ka.

“Mutanen suka dauke ni cikin motarsu. Idan na so in guduwa, da na gudu, amma na ga wadanda suka harbe, na ce idan na bace za su kashe sauran mutanen dake kwance a kasa domn akwai su da dama.

“Kuma da na bace da za a ce ni na kawo masu garkuwan domin ni ne na shigo na karshe. Hakan ya sa na yanke shawarar bin su don in nuna cewa ba ni na kawo su ba. Sannan na yi haka ne domin na ceci rayuka da yawa. Idan kuna tunanin sun dauke ni ne don na ci kudin mutane, bari in gaya muku cewa hakan ba gaskiya bane. Idan na ci kuɗin ku, ku zo wurina ki fada min zan biyaku domin ina da su” a cewar bokan.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments