Daga karshe dai Shigaban Najeriya Bola Ahmed Tinudu ya aika wa Majalisar Dattijan kasar sunayen ministocinsa.
Jerin sunayen da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, bai karanta wa Sanatoci ba, ya tilasta wa majalisar shiga wani zama na sirri.
Jaridar Blueprint ta ruwaito tun misalin karfe 12:15 na rana majalisar ta fara zaman sirrin bayan amincewa da kudurorin da aka gabatar a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Laraba, 26 ga Yuli, 2023.
- Ba mu yadda da hukuncin kotu ba, za mu daukaka kara- Abba Kabir Yusuf
- Gawuna ne ya ci zaben gwamnan Kano-Kotu
Wata majiya mai tushe daga cikin Sanatocin, ta shaida wa jaridar cewa an shiga zaman sirrin ne domin shirya yadda za a tantance wadanda aka nada da kuma tabbatar da su.
Daga yau Alhamis 27 ga watan Yulin 2023 ‘yan majalisan ya kamata su fara hutun mako 6 amma bisa sunayen ministocin da aka aika, ana tunanin a zaman ne za a tattauna domin samar da matsar ko a jinkirta tafiya hutun da mako daya domin tantance ministocin ko kuma su tafi hutun in sun dawo sai su tantamce, kamaryadda majiyar ta tabbatar.
Ga jerin ministocin su 28 kamar haka..
- Abubakar Momo
- Amb. Yusuf Maitama Tuka CON
- Arch Ahmad Dan Giwa
- Bar. Hannatu Musawa
- Chief Uche Nnaji
- Dr. Beta Edu
- Dr. Dorice Uzoka
- David Umahi
- Ezenwa Nnyesom Wike
- Muhammad Badaru Abubakar
- Nasir Ahmed El Rufai
- Rt Hon Aferife Efot
- Nkiru Onyeciyocha
- Hon Olubumi Tunji Ojoh
- Hon. Stella Okuntete
- Hon Uju Kennedy Ohaneye
- Bello Muhammad
- Dele Alake
- Lateef Fabemi SAN
- Muhammad Idris
- Olawale Edu
- Waheed Adebayo
- Hajiya Iman Sulaiman Ibrahim
- Prof. Ali Pate
- Prof. Joseph
- Sanata Abubakar Kyari
- Sanata John Eno
- Sanata Sani Abubakar Danladi
Shugaban ya bayyana cewa akwai sauran sunaye wadanda zai sake aikawa daga baya.