Wasu gungun daliban makarantar sakandire goma a jihar Ogun sun kai lakadawa wani malami mai suna Kolawole Shonuga, wanda ya hana daya daga cikinsu satar amsa yayin jarabawa a makarantar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun Omolola Odutola ya tabbatar da faruwar lamarin a Abeokuta babban birnin jihar inda ya ce an kama daliban.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata a makarantar sakandare ta Isanbi Comprehensive da ke Ilisan-Remo a karamar hukumar Ikenne kamar yadda kafar Channes TV ta ruwaito.
- Sojoji sun gano inda ake kera bindigogi a Kaduna
- Ba mu yadda da hukuncin kotu ba, za mu daukaka kara- Abba Kabir Yusuf
An bayyana cewa wanda abin ya shafa a lokacin da yake kula da daliban SS 1 na makarantar ne ya kama dalibin mai suna Ashimi Adebanjo dan shekaru 18 yana satar amsa tare da kwace takardarsa.
Da alamu sun fusata da wannan mataki, hakan ya sa Ashimi da ‘yan kungiyarsa bayan an rufe makarantar suka yi wa malamin kwanton bauna a kofar makarantar suka yi masa duka.
Wani ganau da ya ba da labarin yadda aka farwa malamin, ya ce daliban ne suka far masa, inda ya kara da cewa daya daga cikinsu mai suna Kazeem Adelaja ya kwada wa malamin sanda a kai yayin da sauran aboka sa suka yi ta dukansa kafin ‘yan sanda su kawo masa dauki tare da kama kimanin goma daga cikin daliban.
Tuni dai aka gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya bisa cin zarafi.
A halin da ake ciki, kungiyar malaman makarantun sakandire (ASUSS) reshen jihar ta bukaci a yi wa malamin adalci bisa cin zarafi da aka yi masa.
Gwamnatin jihar ta kuma yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da sha alwashin ba za ta lamunci ta’asar da dalibai ke yi a fadin jihar ba.