A ranar Litinin da ta gabata ne mazauna yankin Fadikpe da ke birnin Minna fadar jihar Neja suka tsinci wani jariri sabon haihuwa an jefar da shi akan ruwa a rafin yankin.
Wasu mutane daga cikin mazauna yankin ne suka gano jaririn a lokacin da suka ga wani abu yana shawagi a saman ruwa kudaje na sintiri akai.
Sai daya daga cikinsu ya dauki shebur ya ciro abin daga kan ruwan, dubawa ke da wuya sai ya ga ashe jinjiri ne sabon haihuwa domin ko mahaifa ba a ciki daga jikinsa ba.
- Ba mu yadda da hukuncin kotu ba, za mu daukaka kara- Abba Kabir Yusuf
- Gawuna ne ya ci zaben gwamnan Kano-Kotu
Majiyarmu ta Cruisader Radio, Minna ta ruwaito mazauna yankin sun yi Allah wadai da matakin da wanda ta haifi jaririn ta dauka yayin da suka kasa gano wadda ta jefar.
An yi kira ga jami’an tsaro da su nemo wadda ta aikata wannan aika-aikan tare da tabbatar da ta girbi abin da ta shuka.