Thursday, September 21, 2023
GidaDa Dumi-DumiAn kori sarakuna shida a Bauchi kan dalilan siyasa

An kori sarakuna shida a Bauchi kan dalilan siyasa

Gwamnatin jihar Bauchi karkashin Hukumar Kula da Kananan hukumomi ta kori wasu sarakunan gargajiya guda shida bisa zarginsu da shiga harkokin siyasa.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa sarakunan gargajiyar da lamarin ya shafa sun fito ne daga Masarautar Bauchi da Masarautar na jihar.

Mukaddashin sakataren din-din-din na hukumar kula da kananan hukumomin jihar Nasiru Dewu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

“An kori sarakunan shida ne bisa tsoma kansu a siyasar bangaranci, rashin da’a, sare itatuwa, almubazzaranci da dukiyar al’umma da rashin bin doka da oda wanda hakan ya sabawa doka.

“Wadanda aka kora daga masarautar Katagum sun hada da Hakimin Dubi, Aminu Muhammad Malami; Hakimin Azare, Bashir Kabir Umar; Hakimin Tafiya, Umar Omar da Hakimin Tarmasawa, Umar Bani.

“Wadanda abin ya shafa daga Masarautar Bauchi sun hada da Hakimin Beni, Bello Sulaiman da Hakimin kauyen Badara, Yusuf Aliyu Badara,” in ji sanarwar.

Wadanda abin ya shafa daga Masarautar Bauchi sun hada da Hakimin Beni, Bello Sulaiman da Hakimin kauyen Badara, Yusuf Aliyu Badara,” in ji sanarwar.

An umurci sarakunan da aka kora da su mika ragamar gudanar da yankunansu ga sakatarorinsu nan take.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments