Tuesday, September 26, 2023
GidaKunnen GariAn lakada wa wata budurwa duka har lahira a gidan casu

An lakada wa wata budurwa duka har lahira a gidan casu

An tsinci gawar wata budurwa a cikin wani tsohon wurin ninkaya (Swimming Pool) a cikin Cosmila Hotel da ke birnin Awka na jihar Anambra.

Matashiyar mai suna Chinyere Awuda, an gano ‘yar asalin karamar hukumar Idemmili ta kudu ne na jihar ta Anambra.

Majiyoyi sun ce wani Mista Gabriel Chinemere da abokansa ne suka yi wa budurwar dukan ajali a gidan casu na Club Mila da yake mallakin Cosmila Hotel inda dukkansuke zuwa bisa dalilan da ba a sani ba.Majiyar ta kara da cewa, sauran mutanen da ke gidan casun sun yi kokarin ceto matashiyar yayin da ake dukan amma sun kasa domin hatta jami’an tsaron wurin sun gagara yin komai har aka fitar da ita ana dukanta zuwa wurinda aka jefarda ita kafin rai ya yi halinsa.

Bayan an sanar da iyayenta dangane abin da ya sameta, koda suka zo gawarta kawai suka tarar.

Tuni dai jami’an tsaron ‘yan sanda a jihar ta Anambra suka tabbatar da kama wanda ake zargi da aikata wannan aika-aikan.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments