Tuesday, September 26, 2023
GidaKunnen GariKatti shida sun yi wa budurwa fiyade a jihar Neja

Katti shida sun yi wa budurwa fiyade a jihar Neja

Wasu bata garin matasa da ba a tantance ko su waye ba sun yi wa wata budurwa ‘yar shekara 18 fyade a karamar hukumar Lapai da ke jihar Neja.

Lamarin wanda ya faru a ranar Asabar 15 ga watan Yuli da misalin karfe 6 zuwa 7 na yamma, akan hanyar komawar matashiyar gida ne daga islamiyyar da take zuwa koyon haddar Alkur’ani mai girma aka kirata da wata boyayyiyar lamba akan ta same su a makarantar firamare ta Kobo.

A cewar matashiyar, bayan ta isa inda suka ce ta same su da ba ta ga kowa ba sai ta samu wuri ta zauna.

“Lokacin da nake zaune sai na ji sawun mutane suna tafiya,daga kaina ke da wuya sai na ga mutane shida a kaina”.

“Abin da na ji na gaba shine bani wayarki sai na ce waye kai kuma me kake so a wayata, sai wanke ni da mari”.

Da take shaida wa majiyarmu ta  LapaiTV abin da ya faru, ta ce biyu daga cikin wadanda suka aikata mata wannan aika-aika, da suke tattaunawa a gefe ta ji sun kira daya daga cikinsu da Abdullahi, daga nan sai ta ce suka bata wani lemon kwalba.

“Bayan sun tilasta ni in sha lemon, saikuma suka toshe min hanci da kyalle, daga nan ban sake sanin komai ba.” a cewarta.

Mahaifin wanda abin ya shafa Malam Ibrahim Aliyu ya roki mahukunta da su bi masa kadun ‘yarsa.

A baya-bayan nan dai karamar hukumar Lapai na fuskantar matsalolin fyade inda bincike ya nuna cewa ko a makon da ya wuce ma an yi wa wata karamar yarinya fyade.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments