Thursday, September 21, 2023
GidaKunnen GariWani dan POS ya tashi kashe kansa da madarar piya-piya kan bashi

Wani dan POS ya tashi kashe kansa da madarar piya-piya kan bashi

Wani matashi mai sana’ar POS a Yola fadar jihar Adamawa, Umar Faruk Usman a ya sha maganin kashe kwari “piya-piya” da niyyar kashe kansa kan bashin Naira miliyan daaya da dubu dari bakwai da sittin (N1.760m) da wani abokinsa ke binshi.

Umar wanda mazaunin karamar hukumar Yola ta Kudu ne, ya yi yunkurin kashe kansa ne wata babbar kotun yanki dake Yola a ranar Litinin, inda abokinsa mai suna Mustapha Baraya ya kai kararsa kan kudin.

Baraya ya baiwa Umar zunzurutun kudi har Naira miliyan daya da dubu 960 domin gudanar da sana’ar POS amma ya karkatar da kudaden gaba dayansu, Naira dubu N150,000 kawai ya iya mayar mass daga cikin kudin.

Majiyarmu ta News Platform da ake wallafawa a jihar ta ruwaito wanda ya shigar da karar ya yi kokarin ganin ya kwato ragowar Naira miliyan daya da dubu 760 daga hannun Umar amma bai yi nasara ba domin Umar da mahaifinsa sun ci gaba da yaudarar sa bayan hukuncin da kotun ta yanke a watan Feburairun 2023. A ranar 13 ga watan Feburairun wannan shekara ne Baraya ya shigar da karan abokin nasa wannan kotun domin bi masa hakkinsa.

A hukuncin da kotun ta yanke, kotun ta umarce shi da ya mayar da kudin tare da ba shi alfarmar wata guda domin ya shiga duk inda yasan zai samo kudinshi.

Wanda ake kara da mahaifinsa sun sanar da kotun cewa suna da gonar shinkafa da suke ke shirin girbewa,sun yi alkawarin bayan girbi za su mayar da kudin.

Sai dai abin takaicin shi ne wanda ake kara da mahaifinsa sun girbe gonar a asirce ba tare da sanin kotun ba kuma suka ki mayar da kudin.

Kotun dai ba ta da wani zabi da ya wuce bada umarnin saida gidan Umar da mahaifinsa ya ba shi. Bayan an sayar da gidan kan kudi Naira miliyan daya da dubu 100 domin a samu kudin da za a biya bashin, hukuncin bai yi wa Umar dadi ba hakan ya sa ya halarci zaman kotun na ranar Litinin da kwalbar maganin kwari ya bulbula wa cikinsa domin ya kashe kansa.

Sai dai sha ke da wuya sai ya yanke jiki ya fadi nan take inda aka garzaya da shi Asibitin Kwararru na Yola domin ceto rayuwarsa.

RELATED ARTICLES

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

Most Popular

Recent Comments