Rahotanni daga birnin Jalingon jihar Taraba dake Arewa maso gabashin Najeriya sun ce wasu mata masu sana’ar “Burkutu” (Giyar Dawa) sun gudanar zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar dawa wadda da ita suke yin giyar.
A wasu bidiyo da suka bayyana a shafukan sada zumunta da Hausa Daily Times ta samu, matan sun karade manyan titunan Jalingo suna fadin “dawa ya yi tsada komai ya yi tsada”.
Dawa dai a yanzu farashin kowani kwanu ya haura Naira dari 700, yayin da a wasu wurraren ma ake saida kwanu har N900 domin buhunta ya zarce dubu 42.
Tsadar kayan masarufi dai ba a iya dawa ta tsaya ba, kusan farashin dukkan sauran kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a makon da ya gabata.